Matthew 1

1Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. 2Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da ‘yan’uwansa. 3Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram.

4Aram shine mahaifin Amminadab, Amminadab shine mahaifin Nashon, Nashon shine mahaifin Salmon. 5Salmon shine mahaifin Bo’aza ta wurin Rahab, Bo’aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse, 6Yesse shine mahaifin sarki Dauda. Sarki Dauda shine mahaifin Sulaimanu ta wurin matar Uriya.

7Sulaimanu shine mahaifin Rehobo’am, Rehobo’am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. 8Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya.

9Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya. 10Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya. 11Yosiya shine mahaifin Yekoniya da ‘yan’uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila.

12Bayan kwasar su zuwa kasar Babila, Yekoniya shine mahaifin Sheyaltiyel, Sheyaltiyel shine mahaifin Zarubabel. 13Zarubabel shine mahaifin Abihudu, Abihudu shine mahaifin Eliyakim, sannan Eliyakim shine mahaifin Azuru. 14Azuru shine mahaifin Saduku. Saduku shine mahaifin Akimu, sannan Akimu shine mahaifin Aliyudu

15Aliyudu shine mahaifin Ali’azara, Ali’azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. 16Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu. 17Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne

18Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19Mijinta, Yusufu, adalin mutum ne, amma ba ya so ya kunyatar da ita a sarari. Sai ya yi shawara ya sake ta a asirce.

20Yana cikin tunanin wadannan al’amura, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, “Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. 21Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu.”

22Duk wannan ya faru ne domin a cika abinda aka fada ta bakin annabin, cewa, 23“Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel”-ma’ana, “Allah tare da mu.”

24Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala’ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa. Amma Yusufu bai sadu da ita ba sai bayan da ta haifi da. Ya kira sunansa Yesu.

25

Copyright information for HauULB